Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Gabanin Rantsarwa, Shugaban Kasar Kenya Ya Aiko Da Jakada Na Musamman Ga Tinubu Domin Karfafa Alakar Kasashen Biyu

...Ya nemi goyon bayan zababben shugaban kasar kan abubuwan da za su amfani bangarorin biyu A yayin da ranar 29 ga watan Mayu na bikin rants...

...Ya nemi goyon bayan zababben shugaban kasar kan abubuwan da za su amfani bangarorin biyu

A yayin da ranar 29 ga watan Mayu na bikin rantsar da zababben shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ke sake gabato wa, shugaban kasar Kenya, Dakta Williams Ruto, ya aiko da jakada na musamman domin tattaunawa da zababben shugaban kasa kan batutuwan da suka shafi cin moriyar juna tsakanin Nijeriya da Kenya.

Ruto, a cikin wata wasika da ya sanyawa hannu da kan sa, ya taya Tinubu murna kan nasarar da ya samu a rumfunan zabe tare da mika hannun zumunta ga shugaban Nijeriya mai jiran gado.

Hakan ya fito ne a sanarwar da ofishin zababben shugaban kasar ta fitar wanda Abdulaziz Abdulaziz ya sanyawa hannu a ranar Lahadi. 

“A madadin gwamnati da al’ummar kasar Kenya, da kuma a madadina, ina mika sakon gaisuwa da taya murna a gare ka bisa nasarar da ka samu, da kuma al’ummar Tarayyar Nijeriya bisa jajircewarsu da dattakunsu wajen ganin an samu nasarar gudanar da babban zaben 2023.

“Ina son na kuma yaba da kawancen kut da kut da ke tsakanin kasashenmu biyu. Kenya da Nijeriya suna da dabi'u da buri a bangarori daban-daban da suka hada da siyasa, zamantakewa da tattalin arziki, al'adu, musayar diflomasiyya, da kuma hakika rikau na ra’ayi iri daya kan batutuwan da suka shafi nahiya da ma na kasa da kasa”, a wani bangare na wasikar.

Shugaban na Kenya ya kuma yi tayin yin aiki tare da Tinubu domin karfafa doguwar dangantakar dake tsakanin kasarsa da Nijeriya.

“Ina fatan yin aiki tare da kai, domin zage damtse kan manufofin nahiyarmu, da kuma karfafa dankon zumunci da alakar tarihi da abokantaka dake tsakanin kasashenmu da al’ummar kasashen biyu.”

Wakilin shugaban kasar Kenya, wanda kuma shi ne shugaban ma’aikata kuma shugaban ma’aikatan gwamnati na kasar Kenya, Mista Felix K. Koskei, ne ya mika wasikar, a lokacin da yake ganawa da zababben shugaban kasar a karshen mako a Legas.

Koskei ya shaida wa Tinubu cewa burin Ruto shi ne ya hada kai da shugaban Nijeriya mai jiran gado wajen “hada kan Afirka tare da karfafa nahiyar ta hanyar hadin gwiwa da musayar kwarewa”.

A nasa bayanin, zababben shugaban kasa, Tinubu, ya bayyana burinsa na yin aiki tare da shugaban kasar Kenya da sauran shugabannin kasashen Afirka, wajen cin nasarar al’amurran da suka shafi cin moriyar juna.

“Ina da niyyar ci gaba da kiyaye wannan dadaddiyar alakar da ke tsakanin kasashenmu biyu, tare da kuma dorawa daga inda magabatanmu suka tsaya wajen cimma burin gina Afirka mai karfi da ci gaban tattalin arziki mai dorewa”, Tinubu ya shaidawa Jakadan na musamman. 

Tinubu ya yi alkawarin yin aiki tare da Kenya a fannonin bunkasar tattalin arziki, ci gaba da kuma magance matsalar rashin tsaro bisa manufofinsa ga al'ummar Nijeriya.

“Idan muka yi musayar ra’ayi da kuma cudanya a tsakaninmu, hakan zai taimaka wa nahiyarmu. Za a samu damar tattalin arziki domin ci gaban Afirka da kuma tsaro,” in ji shi.

Zababben shugaban kasar ya yi alkawarin kai ziyara ga kasar dake gabashin Afirka a nan gaba domin ci gaba da lalubo hanyoyin da kasashen biyu za su ci moriyar juna da kuma nahiyar Afirka baki daya.



No comments