Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

'Goyon bayan da Tinubu ke nuna wa Akpabio ba zai hana ni neman shugabancin majalisa ba'

  Tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma Sanatan da aka zaÉ“a Abdul’Aziz Yari, ya jaddada buÆ™atarsa ta neman shugabancin majalisar Æ™asar. Daily Tr...

 


Tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma Sanatan da aka zaÉ“a Abdul’Aziz Yari, ya jaddada buÆ™atarsa ta neman shugabancin majalisar Æ™asar.

Daily Trust ta ruwaito cewa sauran waɗanda suke neman wannan matsayi, akwai Gwamna Ebonyi Dave Umahi da Sanata Ali Ndume waɗanda suka janye daga takarar domin marawa wanda jam'iyya ta zaɓa tsohon gwamnan Akwa-Ibom Godswill-Akpabio.

Amma yari ya ce nuna goyon bayan da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Bola Tinubu ya yi kan Godswill, ba zai hana shi takarar ba.

Ya bayyana hakan ne a wani taron masu ruwa da tsaki a tafiyar Tinubu da Shettima wanda shugabanta na ƙasa Khailani Muhammad ya jagoranta a Abuja ranar Asabar.

No comments