Ɗan takarar babbar jam'iyyar adawar Najeriya, Atiku Abubakar ya nuna takaici a kan goyon bayan da Amurka ta bai wa zaɓaɓɓen ...
Ɗan takarar na jam’iyyar PDP ya bayyana mamaki kan tattunawar ta babban jami'in diflomasiyyar Amurka da Tinubu.
A cewarsa, lamarin tamkar wani baki biyu ne ga matsayin da Amurka ta sha bayyanawa a kan zaɓen shugaban ƙasar na Najeriya.
"Wannan lamari yana da wuyar fahimta, ganin cewa Amurka, a matsayinta na tushen kare dimokraɗiyya, kuma an yi mata gamsasshen bayani game da zaɓen 25 ga watan Fabrairu na almara", in ji Atiku.
Babban jagoran adawar na Najeriya dai ya samu ƙuri'a 6,984,520 kwatankwacin kashi 29.07% a zaɓen shugaban ƙasar da ya wuce.
Baya ga Atiku, shi ma ɗan takarar jam'iyyar Labour Peter Obi yana ƙalubalantar nasarar Tinubu a kotu.
Kowannensu yana iƙirarin cewa shi ne ya kamata INEC ta ayyana a matsayin halattaccen ɗan takarar da ya lashe zaɓen.
Atiku ya je kotu
Ɗan takarar shugaban ƙasar na PDP, ya shigar da ƙara gaban kotun ƙorafe-ƙorafe kan zaɓen shugaban ƙasa, yana ƙalubalantar nasarar Bola Tinubu.
Tun da farko, Atiku Abubakar a wani taron manema labarai bayan sanar da sakamakon zaɓen, ya ce dole ne kowa ya ƙalubalanci zaɓen 25 ga watan Fabrairu na 2023.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce "abin da ya faru a zaɓen, fyaɗe ne ga dimokraɗiyya".
A cewarsa, a tarihin ƙasar, shi ne mafi muni da aka taɓa yi, duk da yake, zaɓen wata dama ce ta sake daidaita al'amuran tafiyar da Najeriya".
Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa ta 2023 a yanzu haka da na ci gaba da zaman share fage.
Lauyoyi daga ɓangarorin da ke shari'a a kan zaben na watan Fabrairu, na tafka muhawara a kan buƙatar da Atiku Abubakar ya gabatar, da ke neman kotun ta bari a riƙa nuna zaman sauraron ƙararrakin kai tsaye ta talbijin da rediyo.
Buƙatar da Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima, ta hannun lauyoyinsu ƙarƙashin jagorancin Wole Olanipekun a ranar Larabar nan suka yi watsi da ita, suna cewa yin hakan “tozarta zaman sauraron wannan kotu ce mai ɗaukaka.”
Sun nemi kotun ta kori wannan buƙata, inda suka ce abin da masu ƙorafin ke nema, ba irin abin da kotun za ta iya amincewa da shi ba ne.
Baya ga bayyana buƙatar a matsayin shashanci, lauyoyin sun ce kotun ba gidan raye-raye ko gidan kalankuwa ko filin ƙwallo ba ne da take aiki don nishaɗantar da jama'a.
Sun ce bisa muradin tabbatar da adalci, kamata ya yi kotun ta yi watsi da buƙatar da masu ƙorafi suka gabatar.
©BBC Hausa
No comments