Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Haaland Ya Kafa Tarihin Yawan Jefa Kwallo A Gasar Firimiyar Ingila

Dan wasan gaba na kungiyar Manchester City Erling Haaland ya kafa tarihin yawan cin kwallaye a gasar Firimiyar Ingila, inda a wannan kaka ya...


Dan wasan gaba na kungiyar Manchester City Erling Haaland ya kafa tarihin yawan cin kwallaye a gasar Firimiyar Ingila, inda a wannan kaka ya zura kwallaye 35. 

Dan wasan wanda dan asalin kasar Norway ne, ya zarce yawan kwallaye 34 da ‘yan wasa Alan Shearer da kuma Andrew Cole suka ci a gasar. 

Bayan tashi daga karawar da su ka yi da West Ham a gasar Firimiyar Ingila, ‘yan wasan City sun jeru don jinjina wa dan wasan bisa bajintar da ya yi.  

Haka nan kungiyar ta Manchester City ta samu nasarar jefa kwallo ta dubu 1 a karkashin jagorancin Pep Guardiola. 

Baya ga hakan kuma, kungiyar ta sake taddo tarihin lashe wasanni 9 a jere a gasar da ta kafa tarihin hakan a baya, sannan kuma ta samu nasarar lashe wasa 14 daga cikin 15 na dukkanin gasanni da ta yi a baya-bayan nan. 

No comments