Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

'Haƙƙin ciyar da ɗaurarru a gidajen yari ya koma kan gwamnoni'

  Gwamnatin tarayya a Najeriya ta ce za ta daina ciyar da fursunonin jihohi da ke tsare a gidajen yarin ƙasar daga ƙarshen wannan shekara. T...

 


Gwamnatin tarayya a Najeriya ta ce za ta daina ciyar da fursunonin jihohi da ke tsare a gidajen yarin ƙasar daga ƙarshen wannan shekara.

Ta shawarci jihohin ƙasar su yi cikakken amfani da gyaran fuskar da aka yi wa tsarin mulkin Najeriya a baya-bayan nan, don kyautata rayuwar fursunoninsu.

Wata sanarwa daga ma'aikatar cikin gida, ta ambato Ministan cikin gida, Rauf Aregbesola na cewa matakin, zai fara aiki ne daga ranar 31 ga watan Disamban 2023.

Ya yi shelar cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya sa hannu a kan dokar yi wa tsarin mulkin Najeriya gyaran fuska, abin da ya cire harkar kula da gidajen yari daga ƙarƙashin ikon gwamnatin tarayya kaɗai, zuwa ƙarƙashin ikon haɗin gwiwar gwamnatin tarayya da jihohi.

Don haka in ji sanarwar ma'aikatar cikin gida “Daga ranar 1 ga watan Janairun 2024, gwamnatin tarayya za ta daina ciyar da ɗaurarrun da suka aikata laifuka a jihohi amma ake tsare da su a gidajen yarin tarayya.

Jazaman ne kuma, jihohi su fara yin kasafin kuɗi don ciyar da ɗaurarrunsu da ke gidajen yarin tarayya a daidai lokacin da muke jiran su gina gidajen yari na kansu."

Ya ce matakin zai taimaka wajen ƙara rage cunkoso a gidajen yarin Najeriya.

Ministan ya ce mutanen da suka aikata laifi a jihohi ne fiye da kashi 90% na ɗaurarrun da ke gidajen yarin Najeriya a yanzu.

Ministan cikin gidan ya nanata buƙatar yin cikakken gyaran fuska ga tsarin gudanar da shari'ar laifuka wanda ya ce zai taimaka wajen rage alƙaluma masu tayar da hankali na mutanen da ke jiran shari'a a gidajen yari.

Sanarwar ta ambato ministan na cewa abu ne mai muhimmanci, gwamnatocin jihohi su fara zuba kuɗi cikin harkar kula da gidajen yari.

Amma ministan ya ce, "Abu mafi muhimmanci shi ne buƙatar yi wa tsarin shari'ar laifuka garambawul.

Na sha yin wannan magana, kuma zan ci gaba da yin ta, cewa kashi 70 na mutanen da ake tsare da su a gidajen yari, suna zaman jiran shari'a ne".

A cewar Rauf Aregbesola, wani abin takaici game da haka shi ne "bisa doka ba za mu iya fara ƙoƙarin gyaran halayensu ba, saboda ana ɗaukar su a matsayin marasa laifi, sai dai waɗanda bisa raɗin kansu suka zaɓi shiga".

"Da yawansu sun shafe tsawon lokaci fiye ma da zaman hukunci na laifin da ake zargin sun aikata," Aregbesola ya ce.

Hakan, in ji shi yana sanya su nuna halayyar neman tashin hankali kuma su ne babban ƙalubale ga sha'anin tabbatar da ɗa'a da ikon kula da cibiyoyin tsare mutane a Najeriya.

Ya ce kamata ya yi gwamnatocin jihohi, su yi garambawul ga tsarin gudanar da shari'o'insu, ta hanyar sanya iyaka a tsawon lokacin da ya kamata a kammala shari'a don tabbatar da yin shari'o'i cikin sauri.

Hakan a cewar ministan cikin gida, zai kawo ƙarshen dogon lokacin da ake kwashewa ana shari'a da kuma tsare mutane tsawon lokaci maras iyaka, a kan zargin aikata laifi da kuma rashin adalcin da ke tattare da haka.

An kammala manyan gidajen yarin Kano da Abuja

Dangane da ƙoƙarin rage cunkoso a gidajen yarin, Rauf Aregbesola ya ce daga shi har babban kwanturolan gidan jarin ƙasar, ba su da ikon sakin ɗaurarre.

Ya ce minista da babban kwanturola ba su da ikon tsarewa ko sakin kowa. Ana kai mutane gidajen yari ne da ingantacciyar takardar kotu, kuma ta wannan hanya ce kaɗai ake sakin ɗaurarru.

Haka kuma, in ji shi, shugaban ƙasa ko gwamna suna iya amfani da ikon da suke da shi na yin afuwa wajen sakin ɗaurarre.

Aregbesola ya ce: "Wani babban ƙalubale ɗaya da muke da shi a gidajen yari, shi ne cunkoso, musamman a cibiyoyin tsare mutane a birane inda ake da yawan jama'a, kuma harkokin al'umma ke da wuyar sha'ani, abin da ke janyo yawan aikata laifuka da buƙatar a tsare wasu mutane.

Ya ce suna ƙoƙari wajen shawo kan wannan ƙalubale ta hanyar gina manyan gidajen yari guda shida a dukkan shiyyoyi guda shida na Najeriya.

A cewarsa, an kammala aikin gina sabbin gidajen yari na Kano da Abuja, kuma idan ana samar kuɗi a kai a kai, za a kammala sauran ma.

No comments