A jihar Kaduna ‘yan shi’a magoya bayan Sheikh Ibraheem Zakzaky, ta yi allawadai da matakin da gwamnatin jihar Kadunan ta dauka n...
A jihar Kaduna ‘yan shi’a magoya bayan Sheikh Ibraheem Zakzaky, ta yi allawadai da matakin da gwamnatin jihar Kadunan ta dauka na rushe wata makaranta da kuma asibiti mallakar wasu daga cikin mabiyanta dake Rigasa a garin Kadunan.
Shugaban ‘yan shi’ar reshen jihar Kaduna, Aliyu Umar, da ake yiwa lakabi da Tirmizi, ya shaida wa BBC cewa, basu taba tsammanin irin wannan abu zai ci gaba ba musamman a wurare na ilimi da asibiti inda al’umma ke haduwa na neman lafiya.
Ya ce, ‘’ Mu a matsayinmu na ‘yan uwa musulmi almajiran malam Zakzaky, muna da hakki mu mallaki duk abin da zamu mallaka a karkashin dokokin kasar nan.”
Aliyu Umar, ya ce, ‘’ A yanzu babban matakin da zamu dauka shi ne addu’a Allah (SWA), ya gaggauta daukar mana fansa, na biyu kuma zamu garzaya mu je kotu, kuma an riga ma an kai kara ba a fara shari’a bane.”
Ganau sun ce da tsakar dare ne wasu ma’aikatan hukumar tsara birane ta jihar Kaduna tare da rakiyar jami’an tsaro ne suka isa makaranta da wani asibiti mallakin wasu mambobin kungiyar ‘yan uwa musulmai magoya bayan Sheikh Ibrahim Zakzaky suka rushe.
To sai dai kuma a nata martanin, gwamnatin jihar Kadunan, ta ce an dauki matakin rushe asibiti da makarantar ne saboda wasu dalilai.
Nuhu Garba dan Ayamaka, shi ne kakakin hukumar tsara birane ta jihar Kadunan ya shaida wa BBC cewa, ko da mutum ya gina gini kuma yanada izini daga hukumarsu, daga baya aka gay a sabawa doka bisa dalilai na tsaro, to hakkin hukumar mune mu dauki matakin da ya dace.
Ya ce, ‘’ Na farko an gina wuraren ne ba tare da izini ba, sannan kuma bisa dalilai na tsaro sai da muka aike musu da takarda a kan su a daina gudanar da wasu abubuwa da ake yi a wannan wurare.”
An dai jima ana takun saka tsakanin magoya bayan Sheikh Ibraheem Zakzaky, da kuma gwamnatin jihar Kaduna.
Kazalika wannan lamari ya faru ne yayin da ya rage kasa da ‘yan kwanaki gwamnan jihar Kadunan Malam Nasiru El-Rufai, ya mika mulki ga wanda zai gaje shi.
No comments