Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

HIDIMA GA ALƘUR'ANI: Manyan Malamai, Marigayi Ado Bayero Sun Samu Shaidar Girmamawa

Daga Waziri Mahdi Isa A ranar Lahadi, 21 ga watan Afrilu ne Harkar Musulunci ƙarƙashin jagorancin Shaikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky...


Daga Waziri Mahdi Isa

A ranar Lahadi, 21 ga watan Afrilu ne Harkar Musulunci ƙarƙashin jagorancin Shaikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky ta bada shaidar girmamawa ga wasu manyan malaman addinin Musulunci na Nijeriya da Marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero saboda hidimarsu ga Al-ƙur'ani mai girma.

Manyan malaman sun haɗa da fitaccen malamin ɗariƙar Tijjaniyya, Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi; fitaccen malamin ɗariƙar Qadiriyyah, marigayi Sheikh Nasiru Kabara; da kuma fitaccen malamin ƙungiyar Izala, marigayi Sheikh Jafar Mahmud Adam.

Wakilin ƴan uwa na Harkar Musuluncin na jihar Kano, Sheikh Dr. Sunusi Abdulqadir ne ya miƙa shaidar girmamawar ga wadannan manyan mutane bisa hidimarsu ga Al-ƙur'ani da ma'abotansa.

Wadannan mutane sun samu wannan shaidar girmamawar ne a 'Ranar Mahaddata' karo na 12 da ƴaƴan Harkar musuluncin suka saba gabatarwa a birnin Kano.

A wannan karon, an yaye mahaddatan Al'ƙur'ani kimanin mutum 300, maza da mata.

Bayan gwada haddar mahaddatan da kuma yi musu darasi daga gwanayen Al-ƙur'ani, a ƙarshe an miƙa musu shahadar haddace Al-ƙur'ani mai girma.

No comments