Daga Comrd Abubakar Mai Glass Kujerar shugaban Majalisar dokoki kujera ce wadda ya kamata a samu jajirtaccen mutum mai ilimi, ma...
Daga Comrd Abubakar Mai Glass
Kujerar shugaban Majalisar dokoki kujera ce wadda ya kamata a samu jajirtaccen mutum mai ilimi, mai hakuri, irin su Hon. Nasir Yahaya Daura.
Hon. Nasir Yahaya Daura shi ne ÆŠan majalisa mai wakiltar yankin Daura, kuma shi ne ÆŠan Majalisar da ya yi takarar kujerar Kakaki sau biyu ana kada shi. Saboda hakuri irin nashi ba a taba jin ya yi rigima a kan hakan ba.
Hon. Nasir Yahaya mutum ne mai ilimi wanda ya san mutumcin al'ummar jihar Katsina. A karkashin wakilcinsa yankin Daura ta samu ci gaban da ba ta taɓa samu ba, ya kawo ci gaba sosai, ya samar wa matasa aikin yi.
Yana da kyau mu sani wannan bawan Allahn baya da wani burin da ya wuce ci gaban jihar Katsina. Yana daya daga cikin 'yan majalisun da suke kokari wajen ganin an kawo ma al'ummar jihar ingantaccen ci gaba.
Idan har maganar nagarta da cancanta ake lallai ba mu da kamar Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura
Fatan mu Allah ya sake É—aga darajarsa ya yi masa Kakakin jihar Katsina.
Idan Allah ya yarda ba sai kun yarda ba.
No comments