An yanke wa wani hamshaƙin ɗan siyasar Najeriya, Ike Ekweremadu, da mai ɗakinsa, hukuncin ɗauri a gidan yari bayan kotu a Birtaniya ta sam...
An yanke wa wani hamshaƙin ɗan siyasar Najeriya, Ike Ekweremadu, da mai ɗakinsa, hukuncin ɗauri a gidan yari bayan kotu a Birtaniya ta same su da laifi kan yunƙurin safarar sassan jikin ɗan'adam.
Kotun ta yanke musu hukuncin ne tare da wani likita "mai shigar musu tsakani" bayan sun kai wani matashi Birtaniya daga Lagos.
Yanzu dai, Sanata Ike Ekweremadu zai shafe kusan shekara goma a gidan yarin Birtaniya.
Sanatan mai shekara 60, da mai ɗakinsa Beatrice 'yar shekara 56, sun so a cire wa matashin sashen jikinsa ne da nufin dasa wa 'yarsu Sonia 'yar shekara 25, kamar yadda ma'auratan suka bayyana wa Kotun Old Bailey.
Tun da farko kotu ta samu ma'auratan da likita Dr Obinna Obeta, mai shekara 50, da laifin haɗa baki don ci da gumin mutumin ta hanyar cire ƙodarsa.
Ita ce shari'a ta farko a ƙarƙashin dokokin haramta bautar zamani.
Ike Ekweremadu, wanda alƙalin kotun ya bayyana a matsayin "jigon da ya shirya abin da ya faru gaba ɗaya", zai yi zaman gidan yari tsawon shekara tara da wata takwas.
Haka kuma, ta yanke wa Dr Obinna Obeta hukuncin ɗaurin shekara 10 bayan alƙalin ya gano cewa shi ne ya samo mutumin da zai ba da gudunmawar wanda matashi ne talaka, kuma mai rauni.
Ita kuma matar sanatan na Najeriya, Beatrice Ekweremadu an yanke mata hukuncin ɗaurin shekara huɗu da wata shida saboda yadda ta ɗan sa hannu wajen aikata laifin.
An kuma samu "mai shiga tsakani" Dr Obinna Obeta da matar sanata Ekweremadu, Beatrice, da laifi
A wani zaman yanke hukunci da aka nuna ta talbijin, Mai shari'a Justice Johnson ya nunar cewa Ike Ekweremadu, mutum ne da "ƙimarsa ta yi matuƙar zubewa".
Ya ce: "Masu fasa-ƙwaurin mutane a tsakanin ƙasashen duniya don cire sassa jikin mutum, abin da suke aikatawa wani nau'in bautar da ɗan'adam ne."
Mutumin da suka yi safarar tasa, wani talaka ne mai sana'ar tireda a Lagos, da suka kai shi Birtaniya don a cire masa ƙoda guda ɗaya, da nufin dasa wa 'yar Ekweremadu.
Ya dai tsere ne saboda tsoron mutuwa, inda ya kai kansa ofishin 'yan sanda kimanin shekara ɗaya da ta wuce kuma ya ba da rahoton abin da ya faru, bayan asibitin Royal Free Hospital ya nemi a dakatar da aikin da aka tsara yi a kan kuɗi £80,000.
Kiraye-kirayen a yi sassauci ga Ekweremadu
Manyan 'yan siyasa a Najeriya sun yi ta kiraye-kiraye ga Kotun ta Birtaniya ta nuna sassauci ga Sanata Ike Ekweremadu, ciki har da wani tsohon shugaban ƙasar.
A cikin watan Maris ne, tsohon shugaba Olusegun Obasanjo ya rubuta wasiƙa inda roƙi a yi sassauci ga hukuncin da za a yake wa sanatan Najeriya, Ike Ekweremadu da matarsa.
A wasikar da ya rubuta, Obasanjo ya ce abin da ma'auratan suka yi, ba daidai ba ne kuma babu wata al'umma da za ta lamunci aikata hakan.
Ita ma, Majalisar Dattijan Najeriya, inda Ekweremadu ke aiki, ta bi sahun takwararta Majalisar Wakilai wajen kira ga kotun manyan laifuka ta London a kan ta yi wa sanatan da mai ɗakinsa Beatrice, sassauci.
Matakin majalisar dattijan ya zo ne bayan Sanata Chukwuka Utazi ya gabatar da wani ƙuduri a zaman da aka yi ranar Laraba 3 ga watan Mayu.
Sanata Utazi ya bayyana cewa Ekweremadu, tsohon mataimakin shugaban majalisar dattijan Najeriya ne tsawon shekara 12, kuma tsohon shugaban majalisar dokokin ECOWAS, da ya ba da gudunmawa wajen ci gaban dimokraɗiyyar Najeriya da Afirka ta Yamma.
Ya ƙara da cewa wannan ne karon farko da aka samu Ekweremadu da matarsa da laifi, kuma ba su da wani tarihi na aikata laifi, a cewarsa tun da batun yana Birtaniya, kamata ya yi a yi rangwame wajen yanke hukunci ganin yadda shari'ar tuni ta zama izina ga mutane.
Utazi ya kuma ce ya kamata hukumomin shari'a na Birtaniya su duba irin daɗaɗɗiyar kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin Najeriya da gwamnatin Birtaniya, kuma wannan ne karon farko da majalisar dattijan ƙasar ke miƙa ƙoƙon bara ga gwamnatin Birtaniyar na neman a yi wa Ekweremadu sassauci.
Shuagaban majalisar dattijan, Ahmad Lawan, ya ce ya aika da takarda ga hukumomin shari'a a Birtaniya mako biyu da ya wuce, inda ya nemi a yi sassauci a madadin majalisar dattijan.
-Rahoton BBC Hausa
No comments