Kotun Ƙolin Najeriya ta tabbatar da nasarar Sanata Ademola Adeleke a zaɓen gwamnan jihar Osun. Mai shari'a Emmanuel Akomaye Agim ne ya...
Kotun Ƙolin Najeriya ta tabbatar da nasarar Sanata Ademola Adeleke a zaɓen gwamnan jihar Osun.
Mai shari'a Emmanuel Akomaye Agim ne ya karanto hukuncin da rukunin alƙalan kotun biyar suka saurara, a ƙarar da tsohon gwamnan jihar Gboyega Oyetola ya ɗaukaka.
Daukacin alƙalan ne suka amince da matakin korar shari'ar da Gboyega Oyetola ya ɗaukaka, bayan Kotun Ɗaukaka Ƙara ta rushe hukuncin kotun farko da ta bai wa Gboyega nasara.
Magoya bayan Gwamna Ademola Adeleke da suka halarci zaman yanke hukuncin na ranar Talata a Kotun Ƙoli da ke Abuja, sun kaure da sowa, inda suka shiga rera waƙoƙin 'Ose' da 'Ose'oo' da kuma 'Oserara'.
Tun da farko, Sanata Ademola Adeleke ya wallafa wani saƙo a shafinsa na Tuwita yana cewa "Nasara ta Allah ce".
Kotun Ƙolin ta tabbatar da cewa mai ɗaukaka ƙara ya gaza kafa isassun hujjoji da za su gaskata zarginsa na cewa, an yi aringizon ƙuri'u a zaɓen gwamnan jihar na ranar 16 ga watan Yulin 2022.
Rukunin lauyoyi da ke wakiltar ɓangarorin da ke cikin shari'ar kafin fara zaman yanke hukunci
A cewar dukkan alƙalan da suka saurari ƙarar da aka ɗaukaka, matakin Gboyega na ƙalubalantar nasarar Adeleke, ba shi da tushe balle makama.
A ranar 24 ga watan Maris ne Kotun Ɗaukaka Ƙara ta rushe hukuncin da kotun sauraron ƙararraki kan zaɓen gwamnan Osun ta yanke, inda ta tabbatar da Sanata Adeleke a matsayin wanda ya yi nasara.
Gwamna Adeleke da jam'iyyarsa ta PDP ne suka garzaya gaban Kotun Ɗaukaka Ƙarar suna ƙalubalantar hukuncin ƙaramar kotun da ya rusa zaɓen na watan Yuli.
Sai dai Gboyega Oyetola bai gamsu da hukuncin ba, abin da ya sa ya ɗaukaka ƙara gaban Kotun Ƙolin Najeriya.
A ranar 16 ga watan Yulin shekarar 2022 ne aka gudanar da zaben gwamna a jihar ta Osun inda hukumar zabe ta Najeriya INEC ta ayyana Ademola Adeleke na jam'iyar PDP a matsayin wanda ya samu nasara.
INEC din ta ce Adeleken ya samu ƙuri'a 403,371.
Yayin da Gboyega Oyetola na jam'iyyar APC ya samu kuri'a 375,27 a cewar hukumar zaben ta INEC.
Tuni dai aka fara mayar da martani kan hukuncin Kotun Ƙolin da ya tabbatar da nasarar Gwamna Adeleke, a ciki har da shugaba mai barin gado, Muhammadu Buhari.
A bai wa Adeleke goyon baya - Buhari
Shugaba Buhari ya martaba hukuncin Kotun Ƙolin a kan zaɓen gwamnan jihar Osun na ranar 16 ga watan Yuli da kuma gudunmawar ɓangaren shari'a wajen zurfafa zaman doka da kuma mulkin dimokraɗiyya.
Ya yi kira ga ɓangarorin siyasar jihar su haɗa kai don ganin ci gaban Osun.
Shugaban mai barin gado, ya ce da wannan hukunci na bushewar bakin alƙalami, ya tunasar da 'yan siyasar jihar da magoya bayansu cewa babban aikin da ke gabansu, shi ne bai wa al'ummar Osun damar samun shugabanci nagari.
A cewarsa, hakan zai tabbatar da ƙaruwar arziƙi da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Ya kuma buƙaci dukkan 'yan jihar da mazaunan Osun, musamman manyan 'yan jihar su bai wa gwamnatin Sanata Ademola Adeleke dukkan goyon bayan da take buƙata don ganin shirye-shiryenta na ci gaban ƙasa da manufofi da tsare-tsare da burinta sun cimma nasara.
Da nufin bunƙasa rayuwar ɗaiɗaiku da harkokin kasuwanci a jihar.
Buhari ya ce, "kamata ya yi a ɗauki zaɓe a matsayin wata hanyar cimma buri, don ci gaban al'umma a wani yanayi na kwanciyar hankali da zaman lafiya, maimakon ka-ce-na-ce maras ƙarewa.
Wannan lokaci ne, na bai wa kowa dama a dama da shi, da kuma tabbatar da haɗin kai a jihar Osun bayan kammala shari'a."
No comments