Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Kungiyar Wasan Kwallon Kafa Ta Yi Sabbin Shugabannin A Zamfara

Daga Hussaini Ibrahim Kungiyar wasan kwallon kafa ta jihar Zamfara, wato Zamfara State Football Association ta yi sabbin shugaba...


Daga Hussaini Ibrahim

Kungiyar wasan kwallon kafa ta jihar Zamfara, wato Zamfara State Football Association ta yi sabbin shugabannin a jihar Zamfara.

Shugaban kwamitin gudanar da zaben da uwar kungiyar ta kasa ta turo karkashin jagorancin shugaban na kasa, Alhaji Ibrahim Gusau da ya samu wakilcin shugaban kungiyar na jihar Kano, Rabiu Umar (Ahlan) da sabon shugaban na Jigawa ne suka gabatar da zaben shugabannin na Jihar Zamfara a dakin taron Hukumar bada ilimi bai daya da ke Gusau babban birnin Jihar Zamfara.

Alhaji Rabiu Umar (Ahlan) ya tabbatar da bin tsarin kundin mulkin kungiyar dan kauce ma son rai wajen zaben sabbin shugabannin inda ya umurci shugaban na Jigawa Sabo ya jagoranci gabatar da zaben bisa yadda kundin tsarin kungiyar ya ta nada.

Jim kadan bayan kammala zaben, Sabo Jigawa ya bayyana sakamakon zaben kamar haka, Alhaji Aminu Mamaga a matsayin Shugaban kungiyar na Jihar Zamfara, sai Alhaji Nasiru Muhammad Mataimakin na daya, Alhaji Sabo Tsafe Mataimakin na biyu, sai kuma membobin su shida wadanda suka hada da , Abdullahi Umar Bungudu, Kabir M. Rabiu Maru, Abubakar Muhammad Birnin Magaji, Musa Muhammad Shinkafi, Yahuza Maihaja, Tata Mafara, sai kuma Abubakar Musa Bakura. Wadannan sune sabbin shugabannin da aka zaba domin ciyar da kungiyar ci gaba a cikin Jihar Zamfara, inji Sabo Jigawa.

A jawabinsa Shugaban kungiyar na Kasa da Alhaji Rabiu Ahlan ya wakilta ya yi kira ga sabbin shugabannin da su tashi tsaye wajen ci gaban kungiyar ta kowanne sashe.

Rabiu Ahlan ya kuma yi kira ga sabuwar Gwamnatin Jihar Zamfara da su taimaka ma 'yan wasan kwallon kafa don tsamo su daga cikin mawuyacin halin da da suke cikin don tsakani ga Allah 'yan wasan kwallon kafa suna neman dauki ga su da kwazo matsalolin yau da kullum sun tauye su don Allah a taimaka musu, inji Rabiu Alhalan.
 
Shima a nasa jawabin Shugaban Alhaji Aminu Mamaga ya tabbatar da cewa, za su ba marada kunya wajen samun nasarar kungiyar da 'yan kwallon kafa da fadin Jihar ta Zamfara.

Alhaji Aminu Mamaga ya kuma mika godiyarsa ga membobin kungiyar da suka ga cancantar su da su jagoranci kungiyar.

Godiya ta musamman ga wakilan na kasa, Alhaji Rabiu Ahlan da Sabo Jigawa da suka ga batar da zaben da kuma Shugaban kungiyar na kasa Alhaji Ibrahim Musa Gusau akan yadda ya ke sanya mutanen mu cikin kwamitocin wasanin na kasa da kuma taimaka musu a harkar wasanni. 

No comments