Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Majalisar Dattawa Ta Amince Da Kudurin Ɗaurin Rai-Da-Rai Ga Masu Haɗa Abubuwan Fashewa

Majalisar dattawan Najeriya ta amince da wani kudirin doka da ke ba da shawarar ɗaurin rai-da-rai, ba tare da zaɓin tara ba ga masu kera abu...

Majalisar dattawan Najeriya ta amince da wani kudirin doka da ke ba da shawarar ɗaurin rai-da-rai, ba tare da zaɓin tara ba ga masu kera abubuwan fashewa a ƙasar.

Zartas da kudurin dokar a ranar Laraba ya biyo bayan nazari tare da amincewa da wani rahoton kwamitin majalisar dattawa kan albarkatun ƙasa da bunkasa karafa.

'Yan majalisar dai sun ce masu aikata laifuka na ƙara amfani da hanyoyin zamani wajen haɗa abubuwan fashewa.

Sun ce ‘yan kunar bakin-wake sun kashe gwamman ‘yan Najeriya ta hanyar amfani da ababen fashewa.

Majalisar wakilai za ta yi muhawara kan kudirin dokar kafin a mika shi ga shugaban ƙasa domin amincewa.

Yawancin abubuwan fashewa da maharan ke amfani da su, an ce an yi su ne ta amfani da wasu sinadarai.

No comments