Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Makarantar Mu'azu Bin Jabal Littahfizil Kur'an Ta Yi Bikin Saukar Karatun Alkur'ani Karo Na Farko

Daga Idris Umar, Zariya Madarasatul Mu'azu Bin Jabal Littahafizil Kur'an dake Zangon Shanu Hayin Shehu Zariya a karamar ...


Daga Idris Umar, Zariya

Madarasatul Mu'azu Bin Jabal Littahafizil Kur'an dake Zangon Shanu Hayin Shehu Zariya a karamar hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna ta yi bikin saukar karatun Alkur'ani karo na farko

Makarantar an kafa ta ne tun shekara ta 2014 karkashin jagorancin wasu bayin Allah masu kishin Addinin Islama cikinsu akwai Farfesa Hamza Mani da Dakta Yakub A.A Wakili da Malam Rudwan Muhammed.

A ranar 10 ga Shawwal, 1444(h) wanda ya yi daidai da 30 ga watan 4 na 2023  makarantar ta yi bikin saukar karatun Al'kur'ani karo na Farko.

Daga cikin daliban da aka yi walimar dominsu akwai dalibai 6 da suka haddace Al'kur'ani akwai kuma dalibai 33 da suka yi sauka duk a wannan lokacin kuma a makarantar.

Shugaban shiyya na makarantar Malam Shamsuddin Jibrin ya bayyana irin nasarori da makarantar ta samu a zuwa wannan lokacin.

Shugaban ya ve kafa makarantar an sami hazikan dalibai gami da mahaddata Al'kur'ani mai girma a yankin.

Ya ce an sami rassa guda Uku (3) da ya hada da sashen Islamiyya da sashen Hadda da sashen matan aure.

An fara da dalibai kadan amma yanzu makarantar tana da akalla dalibai dari uku da hamsin (350). 

Shugaban shiyyar ya bayyana rashin biyan kudin makaranta akan lokaci na daga cikin kalubalen da makarantar ke fuskanta a halin yanzu sai muhalli da kayan koyar da sana'ar hannu ga dalibai da sauran gyare-gyaren da ba a rasa ba.

Hakan yasa Malamai da Sarakunan da suka gabatar da wa'azi a wurin suka yi kira ga iyaye da su kara dagewa wajen biyan kudin makarantar.

Haka zalika Malaman sun yi kira ga dalibai da su zama masu aiki da abin da suka karanta dokin hakan ne zai nuna suna tsoran Allah.

Makarantar Mu'azu Bin Jabal reshen Zango yanzu haka tana da rassa a Hayin Liman wanda yake da rassa guda 3 akwai sashen Hadda da sashen Islamiyya da sashen matan Aure.

Bincike ya tabbatar da cewa daga abin da makarantar ke samu ne suka yi wannan kokarin.

Bisa haka ne hukumar makarantar ta mika sakon godiya ga jama'ar dake bayar da gudummawa ciki har da kungiyar mata da ake kira da Women Intellectuals bisa kokarin da suke nunawa a wannan makarantar.

Bincike ya kara tabbatar da cewa makarantar Mu'azu Bin Jabal ta fi kowacce makarantar dake yankin saukin kudin makarantar.

A don haka Malamai da Sarakuna da kungiyar iyaye (PTA) na makarantar suka yi jinjina ga ilahirin jama'ar wannan Anguwa bisa kokarin da nuna kishin da suka yi ga makarantar.

An karrama wasu muhimman mutane a wajalen taron daga ciki akwai Kanar Abdulkareem Usman da Sheikh Abba Dewu da Hajiya Hauwa Abdulkarim da wasu muhimman mutane bisa kokarin da suke bayarwa a bangaren ci gaban makarantar a lokutan baya da yanzu ma.
Malam Abubakar Abba Dewu shi ne Shugaban makarantar baki daya a jawabinsa ya yi godiya ga dukkan wanda suka bayar da dukiyarsu da lokutansu domin taimakawa wannan makarantar kuma ya yi fatan Allah ya saka masu da aljanna.

Daga cikin manyan baki akwai Sheikh Salisu Abubakar Limamin masallacin ITN da Kanar Usman Abdulkarem da wakilin Sarkin Zazzau Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, Alhaji Bagudu da dai sauran manyan baki daga bangarori da dama.

An yi taro lafiya an tashi lafiya.

No comments