Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Man City Ta Casa Real Madrid A Gasar UCL

Manchester City ta kai zagayen karshe a Champions League, bayan da ta doke Real Madrid 4-0 ranar Laraba a Etihad. City ta fara c...


Manchester City ta kai zagayen karshe a Champions League, bayan da ta doke Real Madrid 4-0 ranar Laraba a Etihad.

City ta fara cin kwallo ta hannun Bernardo Silva a minti na 23 da fara wasa, sannan ya kara na biyu minti 14 tsakani.

Hakan ya sa Silva ya zama dan wasa na uku da ya ci Real Madrid kwallo biyu ko fiye da hakan a daf da karshe a Champions League.

Lionel Messi ne ya fara wannan bajintar a 2011, sannan Robert Lewandowski ya zaman a biyu a 2013.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Eder Militao ya ci gida, sannan Julian Alvarez ya kara na hudu a karawar ta hamayya.

Karo na biyu da dura kwallaye da yawa a ragae Real Madrid a Champions League, bayan wanda Liverpool ta yi mata a watan Maris din 2009.

Manchester City ta kai zagayen gaba da cin Real Madrid 5-1 gida da waje kenan a babbar gasar tamaula ta zakarun Turai

Ranar Talata 9 ga watan Mayu Real Madrid da City suka tashi 1-1 a wasan farko a daf da karshe a Sifaniya.

Da wannan nasarar Pep Guardiola ya ja ragamar cin wasa na 100 a Champions League, kuma shine na uku a wannan kwazon, bayan Carlo Ancelotti mai 107 da kuma Sir Alex Ferguson 102.

A kakar bara Real ce ta fitar da City a irin wannan matakin da cin 6-5 gida da waje, sannan ta je karawar karshe ta kuma lashe kofin na 14 jimilla.

Pep Guardiola ya dauki Champions League biyu a matakin koci a Barcelona a 2009 da kuma 2011, amma ya kasa ci a Bayern Munich da Manchester City.

Haka kuma kocin dan kasar Sifaniya, mai rike da Premier League na bara, ya kai City karawar karshe a Champions League, inda Chelsea ta dauka kaka biyu da ta wuce.

City na fatan daukar kofi uku a bana, bayan da za ta buga wasa karshe a FA Cup da Manchester United.

Haka kuma City na neman cin wasa daya daga ukun da ke gabanta ta lashe Premier League na kakar nan, za ta fuskanci Chelsea da Brighton da Brentford.

Ranar 10 ga watan Yuni za a buga wasan karshe a Champions League tsakanin Manchester City da Inter Milan.

Wannan shine karon farko da za su fuskanci juna a babbar gasar tamaula ta zakarun Turai.

Inter ta kawo wannan matakin, bayan da ta ci AC Milan 3-0 gida da waje, karon farko da ta kai fafatawar karshe tun bayan 2010.

Manchester City ba ta taba cin Champions League ba a tarihi, wannan shine karo na biyu da Guardiola ya kai kungiyar wasan karshe a gasar. 


No comments