Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Masarautun Kano Mahadi Ka Ture Kuma Allah Ba Zai Kawo Wannan Mahadin Ba -Ganduje

  Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce babu wani mahaluki da zai taba sabbin masarautun jihar guda 4 da ya kirkiro domin haifar d...

 


Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce babu wani mahaluki da zai taba sabbin masarautun jihar guda 4 da ya kirkiro domin haifar da ci gaba a kowanne sashe na jihar. 

Ganduje ya shaidawa taron ma’aikatan jihar da suka halarci bikin ranar ma’aikata ta duniya cewar Allah ba zai bai wa wani mahaluki damar ruguza su ba, kamar yadda wasu ke hasashe yanzu haka. 

Gwamnan mai barin gado ya bayyana masarautun a matsayin wani ginshiki na hadin kai, ci gaba da kuma inganta rayuwar jama’ar jihar. 

Ganduje ya ce a wannan lokaci duk wanda ya ziyarci sabbin masarautun zai ga irin ci gaban da aka samu, wadanda suka dada daga darajar al’adun jama’ar dake yankunan da kuma girmama su. 

Gwamnan ya bayyana cewar ko da basa cikin gwamnati, za su ci gaba da yin addu’o'i ga Ubangiji domin kare wadannan masarautu. 

Wadannan kalamai na gwamnan mai shirin barin gado na zama tamkar wani martani ne ga kalaman tsohon gwamnan jihar Rabiu Musa Kwankwaso, wanda yake cewa sabuwar gwamnati da za ta karbi mulki a karshen wannan watan za ta duba makomar sabbin masarautun da kuma tube tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na 2 da gwamna Ganduje ya yi. 

Tuni aka samu rarrabuwar kawuna a jihar dangane da wadannan kalamai tsakanin masu goyan bayan sabbin masarautun da kuma wadanda ke ganin cewar ba a yi wa tsohon Sarki Muhammadu Sanusi adalci wajen tube shi da kuma karkasa masarautar Kanon ba. 

No comments