Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Na Sha Suka Ne Kawai Saboda A Cusguna Wa Mijina - Turai 'Yar'adua

  Hajiya Turai 'Yar'adua, uwargidan tsohon shugaban Najeriya ta bayyana mijinta Umaru Musa 'Yar'adua a matsayin mutum mai sa...

 


Hajiya Turai 'Yar'adua, uwargidan tsohon shugaban Najeriya ta bayyana mijinta Umaru Musa 'Yar'adua a matsayin mutum mai sauƙin kai da matuƙar gudun duniya.

"Ko shugabanci, haka nan Allah ya kawo shi, amma ba don yana buri ba".

Ta dai bayyana haka ne yayin zantawa ta musamman da BBC Hausa ranar Juma'a, a wani ɓangare na cikar maigidanta shekara 13 da rasuwa.

Uwargidan tsohon shugaban Najeriya, ta ce a kullum tana tuna rayuwarsu da maigidan nata, "kawai dai bambancin yau (ranar cikarsa shekara 13 da rasuwa) ina jin daɗi saboda yadda mutane suke taruwa ana karatu(n Alƙur'ani), ana yi masa addu'a".

Turai 'Yar'adua ta ce ta fara kukan rashin mijinta Umaru ne ranar da ta dawo daga tafiya, amma babu wanda ko ya tuntuɓe ta don jin yaya ta sauka.

Uwargidan tsohon shugaban Najeriya Umaru Musa 'Yar'adua, da ya rasu a kan karagar mulki a shekara ta 2010, ta ce an yi ta sukar ta ne a lokacin mulkin mijinta saboda kawai wasu su huce haushin da suke ji game da shi.

Ta ce matuƙar shugaban ƙasa zai hana aikata ba daidai ba. Kuma ba ruwansa da shiga wasu harkoki na rashin gaskiya, da za a yi amfani da su wajen sukar lamirinsa, to uwargidansa za a ɗora wa karan tsana.

Uwargidan tsohon shugaban ƙasar wadda ta bayyana cewa ba ta da wani buri na shiga harkokin siyasa, ta shawarci Sanata Remi Tinubu, uwargidan zaɓaɓɓen shugaban Najerya Bola Ahmed Tinubu da cewa ta yi haƙuri game da ƙalubalen rayuwar da za ta fuskanta nan gaba.


-BBC Hausa

No comments