Alkaluman mutanen da rikicin Sudan ya raba da muhallansu ya ninƙa zuwa sama da mutum 700, 000, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya. Ƙaruwar mu...
Alkaluman mutanen da rikicin Sudan ya raba da muhallansu ya ninƙa zuwa sama da mutum 700, 000, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya.
Ƙaruwar mutanen da ke guje wa muhallansu ya sanya fargaba kan yaɗuwar faɗan duk da tattaunawar tsagauta buɗe wuta da ake yi a Saudiyya.
Ana ci gaba da kai hare-hare ta sama a Khartoum, babban birnin ƙasar.
Mutane da dama sun tserewa gidajensu saboda fargabar hare-hare.
Khartoum na da al'umma kusan miliyan 5.4, sai dai an ɗaiɗaita birnin mai cike da zaman lafiya a baya tun bayan ɓarkewar faɗa a ranar 15 ga watan Afrilu.
Ana gudanar da faɗan ne tsakanin sojojin ƙasar da Janar Abdel Fattah al-Burhan ke jagorata da kuma dakarun RSF ɓangaren Janar Mohamed Hamdan Dagalo, wanda aka fi sani da Hemedti.
Sama da mutum 600 ne aka kashe kawo yanzu tare da jikkata 5,000.
No comments