Cristiano Ronaldo ya zama dan wasa na daya mafi karbar albashi a duniya a karon farko tun shekarar 2017 bayan komawarsa kungiyar Al Nassr ta...
Cristiano Ronaldo ya zama dan wasa na daya mafi karbar albashi a duniya a karon farko tun shekarar 2017 bayan komawarsa kungiyar Al Nassr ta kasar Saudiyya.
Mujallar Forbes ta ce dan wasan na Portugal mai shekara 38 ya samu Yuro miliyan 108.7 a cikin watanni 12 da suka gabata.
Rahotanni sun ce kwantiraginsa da Al Nassr ya kai sama da Yuro miliyan 200 a duk shekara.
Kaftin din Argentina wanda ya lashe gasar cin kofin duniya Lionel Messi, shi ne na biyu a jerin sunayen da mujallar Forbes ta fitar, inda ya samu Yuro £103.9.
No comments