Daga Abdullahi Idris, Bauchi Rundunar 'yan sandan Nijeriya a jihar Bauchi ta bayyana nasarar cafke wani korarren kurtun dan...
Daga Abdullahi Idris, Bauchi
Rundunar 'yan sandan Nijeriya a jihar Bauchi ta bayyana nasarar cafke wani korarren kurtun dan sanda mai suna Muhammed Jawat, mai shekaru 27 tare da wasu mutum biyu da suka hada da Muhammed Ahmed dan shekaru 27 gami da Husaini Ahmad mai shekaru 19 da laifin aikata fashi da makami.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Ahmed Muhammed Wakili shi ne ya bayyana hakan a kafafen yada labarai a Jihar Bauchi .
Ya ce bayan rundunar yan sandan ta sami labarin sirri game da 'yan fashin, ta kai masu samame a tashar mota ta garin Jama'are inda ta yi nasarar damko su
'Yan sanda sun kuma sami 'yan fashin da wata karamar bindigar hannu kirar gida, da kuma kwalson alburusai da babu komai a ciki.
Kakakin rundunar ya bayyana cewa wadanda ake zargin sun tabbatar da aikata laifin da ake zarginsu da shi na aikata fashi da makami, inda ya ce bayan kammala binciken 'yan sanda, za su tasa keyarsu zuwa gaban kuliya domin yanke musu hukunci daidai da abin da suka aikata.
No comments