Sanata mai wakiltar Borno ta kudu, Sanata Ali Ndume, da Sanata Barau Jibrin daga jihar Kano, sun janye daga takarar kujerar shug...
Sanata mai wakiltar Borno ta kudu, Sanata Ali Ndume, da Sanata Barau Jibrin daga jihar Kano, sun janye daga takarar kujerar shugaban majalisar dattawa.
Jiga-Jigan sanatocin jam'iyyah mai mulki watau APC sun hakura da takara ne jim kaÉ—an bayan gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi ya janye, kuma ya marawa Godwill Akpabio baya.
A wani taro da ya gudana a gidan gwamnan Ebonyi da ke Abuja, Umahi yace ya hakura da takara, kuma ya koma bayan wanda APC ta zaɓa a matsayin ɗan takarar maslaha, kamar yadda jaridar The Cable ta rahoto.
Legit.ng Hausa ta kawo maku rahoton cewa Tinubu da APC sun amince da Akpabio ya zama shugaban majalisar Dattawa, Barau Jibrin kuma ya zama mataimakinsa.
Ndume da Barau sun bi sahun Umahi
Da yake tabbatar da janyewarsa, Sanata Ndume yace zai jagorancin yaƙin neman zaben Akpabio a matsayin shugaban majalisar dattawa ta 10 da za'a rantsar a watan Yuni.
Jaridar Tribune ta ruwaito Ndume na cewa:
"Ba janye wa daga takara kaɗai na yi ba, ni zan jagorancin yakin neman zaben Akpabio saboda shi zababben shugaban ƙasa ya marawa baya kuma mun ji mun miƙa wuya domin kishin jam'iyya."
"Asiwaju yace ni ya kamata na jagoranci kamfen Akpabio, kun ga yanda yayi kaurin suna. Saboda haka muna bayan tikitin Akpabio da Barau."
Akpabio ya maida martani
Da yake martani, Akpabio ya ƙara gode wa takwarorinsa bisa goyon bayan burinsa na zama shugaban majalisar dattawa. Yace:
"Na miƙa komai ga Allah kuma a koda yaushe na kance In Sha Allah, idan Allah yaso abinda ya tsara ne zai faru a Najeriya."
Hukumar sojin Najeriya ta ce ta shirya tsaf zata muƙushe duk wanda yayi yunkurin kawo cikas ranar 29 ga watan Mayu, 2023.
No comments