Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Sarkin Yakin Maradin Zazzau Ya Yi Kira Ga Matasa

Daga Idris Umar, Zariya Sarkin yakin Maradin Zazzau (Dawa Kabiru) ya yi kira ga matasa da su zama masu son zaman lafiya a tsakan...


Daga Idris Umar, Zariya

Sarkin yakin Maradin Zazzau (Dawa Kabiru) ya yi kira ga matasa da su zama masu son zaman lafiya a tsakaninsu da juna.

Kabiru ya yi wannan kiran ne a yayin da yake zantawa da manema labarai a gidansa dake Samarun Zariya.

Kafin ya karkare bayanin nasa ya kara da cewa kamar yadda Maradin Zazzau Alhaji Muhammad Haruna Jumare ke yawan janyo hankalin matasa akan zaman lafiya ya ce haka suma za su wakilce shi a kowanne lokaci a wannan bangaren domin ci gaban kasar Zazzau karkashin Sarki Mai Martaba Uban kasa Ambassada Ahmed Nuhu Bamalli.

Karshe ya ce ya kamata matasa su kaucewa duk wani abin da zai kawo tashin hankali a tsakanin juna, inda ya ce maimakon haka a nemi sana'ar hannu komin kankantarta hakan na maganin abubuwa masu yawa a rayuwar matashi.

Ya kuma yi yabo ga jami'an tsaro bisa kokarin da suke yi na samar da zaman lafiya a cikin al'umma dare da rana.

Da Sarkin yakin ya koma bangaren 'yan siyasa kuwa kira ya yi gare su da su zama masu tausayi ga al'umma tare da kawo masu kudurorin da zai cire talauci a tsakanin al'ummarsu.

Kuma ya yi addu'a ga sabbin shugabanni da za su karbi karagar mulki da Allah ya sa su fara cikin nasara.

No comments