Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Taƙaddama ta kaure kan batun miƙa mulki a Zamfara

  Taƙaddama ta kaure tsakanin gwamnatin APC mai barin gado da kuma ta jam'iyyar PDP mai zuwa a jihar Zamfara. Lamarin na zuwa ne, bayan ...

 


Taƙaddama ta kaure tsakanin gwamnatin APC mai barin gado da kuma ta jam'iyyar PDP mai zuwa a jihar Zamfara.

Lamarin na zuwa ne, bayan zargin cewa ƙananan kwamitocin karɓar mulki na gwamnati mai jiran gado suna wuce gona da iri.

Gwamnatin jihar ta yi zargin cewa ƙananan kwamitocin na zuwa ma'aikatu suna bincike tare da karɓar bayanai, wanda a cewarta abu ne da bai dace ba, kuma ya saɓa wa Tsarin Mulki.

Gwamnatin APCn ta ce abubuwan da kwamitocin ke yi, tamkar 'kafa gwamnati ne a cikin gwamnati', inda ta buƙaci su jira har sai an miƙa musu mulki.

Kwamishinan yaɗa labaran jihar, Ibrahim Dosara, ya shaida wa BBC cewa ƙananan kwamitocin sun kasance suna bin ma'aikatu suna karɓar bayanai da gudanar da bincike tare da karɓar bayanan asusu-asusun ajiya na ma'aikatun domin yin bincike.

Dosara ya ce muddin kwmitocin ba su daina abin da suke yi ba, to hakan zai iya haddasa rikici, inda ya buƙaci su bari har sai sun hau kan mulki.

"Duk bayanai da ake buƙata, ma'aikatun sun tattara tare kuma da miƙa wa kwamitin bayar da mulki, inda za su bai wa gwamna mai ci wanda shi kuma zai kira gwamna mai shigowa, su zauna inda zai miƙa masa," in ji Dosara.

Sai dai shugabannin kwamitin karɓar mulki na gwamnatin PDP mai jiran gado a jihar Zamfara, ba su mayar da martani game da wannan zargi ba.

Amma Alhaji Muhammad Kabir Janyau, mamba a ɗaya daga cikin ƙananan kwamitocin karɓar mulkin, ya ce takaicin barin mulki ne ke sa gwamnatin mai barin gado yin magiya.

Kabir Janyau ya ce tattara bayanai da miƙa su daga gwamnati mai barin gado zuwa gwamnati mai zuwa, abu ne da aka saba yi wanda ana yin haka ne domin ita gwamnati mai zuwa ta san daga ina za ta fara.

Ya ce watakila suna tsoron irin ayyukan da suka aiwatar da suka saɓa doka ne.

Irin wannan sa-in-sa da ke faruwa tsakanin gwamnati mai barin gado da mai jiran gado a jihar Zamfara na faruwa a wasu jihohin Najeriya musamman a wajen da mulki ya kuɓuce wa wata jam'iyya zuwa wata.

Ko a kwanakin baya ma, an samu irin wannan takun-sakar tsakanin gwamnatin NNPP mai jiran gado da kuma ta APC mai barin gado a jihar Kano.

No comments