Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Wane ne Honorabul Ibrahim Garba?

Daga Idris Umar, Zariya Da yawa ana samun tambaya game da wannan matashi a gida da waje domin sanin hakikaninsa, to a yau mun zo...


Daga Idris Umar, Zariya

Da yawa ana samun tambaya game da wannan matashi a gida da waje domin sanin hakikaninsa, to a yau mun zo mako da tarihin Honorabul Ibrahim Garba a takaice.

Shi dai Honorabul Ibrahim Garba an haife sa ne a ranar 15 ga watan Satumbar shekarar 1995 a Tudun- Wada Zaria da ke karamar hukumar Zariya a jihar Kaduna.

Ya yi karatun sa na Firamare a makarantar A.B.U Staff School da ke Kongo daga shekarar 2000 zuwa shekarar 2004, ya yi karamar Sakandire ta Demonstration Secondary School A.B.U Zariya daga shekarar 2006 zuwa 2009, babbar Sakandire ta Demonstration Secondary School daga shekarar 2009 zuwa 2012. 

Honorabul Ibrahim Garba daga nan ya yi National Diploma a fannin Computer Science a Nuhu Bamalli Polytechnic da ke Zariya daga shekarar 2012 zuwa 2014, daga nan ya yi digiri a fannin Computer Science a jami'ar National Open University, Kaduna Study Center inda ya gama da Second Class Lower Division.

Bayan gama karatunsa na digiri, Ibrahim Garba ya yi aikin yi wa kasa hidima a jihar Bauchi daga watan Yunin shekarar 2019 zuwa watan Yunin shekarar 2020.

Bayan aikin yi wa kasa hidima, Ibrahim Garba yana aiki a Madalla College of Health Science and Technology da ke Zariya wanda ya fara a shekarar 2016 zuwa yanzu, yana kuma aiki a Halim College of Health, Science and Technology da ke Minna a jihar Neja da kuma karamar hukumar Ikara da ke jihar Kaduna daga shekarar 2019 zuwa yanzu.

A yanzu haka yana karatunsa na digiri na biyu ne a fannin Information Management a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya. 

Ibrahim Garba ya samu lambobin yabo da dama, a cikinsu akwai wadda Northern Youth Council (NYC) ta bashi a matsayin "Icon of Excellence and Jagaban Matasan Arewa" 

Ya samu lambar yabo daga Association of Nothern Nigeria Students (ANNS) a matsayin "Icon of Humanitarian Service" a Arewa House da ke Kaduna.

Ya sake samun lambar yabo daga National Association of Nigerian Students (NANS) a matsayin "Icon of Community Development" kuma kungiyar ta dalibai ta yi masa girmamawa ta kasa a matsayin Grand Commander of Nigerian Students GCNS.  

Taskira Newspaper ta girmama shi a matsayin 'most caring citizen' in Zaria a shekarar 2017.

A yanzu haka wani jigo ne a cikin kungiyar Arewa Youth Development shiyyar karamar hukumar Zariya.

Haka nan kuma Arewa Elite Magazine ta bashi lambar yabo ta "Outstanding Youth of the Year 2018" Zariya, Nijeriya.

No comments