Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Yadda Matawalle Ya Kwashe Biliyoyin Naira Don Yin Aikin Bogi A Fannin Lafiya A Zamfara

Daga Musa Saleh Zurmi Cikin ƙasa da wata guda ya fice daga gidan gwamnati, bayanai na ci gaba da fitowa kan yadda gwamnan jihar ...


Daga Musa Saleh Zurmi

Cikin Æ™asa da wata guda ya fice daga gidan gwamnati, bayanai na ci gaba da fitowa kan yadda gwamnan jihar Zamfara mai barin gado Bello Mohammed Matawalle ya amince tare da biyan cikakken kuÉ—i na ayyukan da aka yi na bogi ko kuma aka yi watsi da su tun da farawa. 

Wani bincike da aka gudanar a baya-bayan nan ya nuna yadda Gwamna mai barin gado ya raba biliyoyin Naira ga ‘yan kwangilar gine-gine da gyare-gyaren masaukan Gwamna a faÉ—in Æ™ananan hukumomi 14 na jihar.

Binciken bayanan ayyukan bogin ya fallasa sunayen wasu ’yan kwangilar a matsayin 'yan'uwa, da kuma makusantan Gwamna Matawalle.

Gwamnatin jihar Zamfara ƙarƙashin Gwamna Bello Mohammed Matawalle a cikin shekarar 2020 a lokacin annobar COVID-19 ta tunkari gwamnatin tarayya domin biyan Naira biliyan biyu a matsayin kuɗin gina cibiyar COVID-19. Gwamnatin jihar ta bayyana cewa tana buƙatar kuɗaɗen ne domin gyara, sabuntawa, da kuma siyan magunguna ga asibitocin faɗin jihar.

A watan Janairun 2023, gwamnatin tarayyar Nijeriya ta bai wa gwamnatin jihar Zamfara zunzurutun kuɗi har naira biliyan biyu kamar yadda ta buƙata. An bayar da kuɗin ne domin gyarawa, sabuntawa, da kuma samar da magunguna ga asibitocin faɗin jihar.

Wata takarda daga ma’aikatar lafiya ta jihar Zamfara ta fallasa yadda Gwamna mai barin gado ya amince da biyan Naira 323, 029, 163. 88 ga wani É—an kwangilar DBC Nigeria Construction and Mech. Company Limited domin gyarawa da sauya fasalin babban asibitin Gummi.

Ziyarar da aka kai babban asibitin garin na Gummi ya nuna akasin haka. Asibitin yana cikin mummunan yanayi tare da lalacewar kayayyakin aikin dake cikinsa. Babu wani aiki da ake ci gaba da yi duk biyan miliyoyin naira da gwamnan ya yi.

An amincewa wani kamfani mai suna New Horizon LTD domin gyarawa da sauya fasalin babban asibitin ƙaramar hukumar Tsafe. Gwamnatin Matawalle ta saki zunzurutun kuɗi har Naira 91,000,000 ga ɗan kwangilar. Asibitin dake Tsafe har yanzu yana nan a cikin mummunan hali.

A shekarar 2020, A.H.B Modandi Global Services ya samu kwangilar gina cibiyoyin lura da lafiyar mata da ƙananan yara guda 14 a faɗin ƙananan hukumomi 14 na jihar. An biya jimillar kuɗi 352, 171, 190. 00, duk da haka babu irin waɗannan cibiyoyin a asibitocin jihar.

A ranar 2 ga Nuwamba, 2020, wannan dai kamfani na A.H.B Modandi Global Services an sake ba shi kwangilar siyan kayayyakin aikin asibiti domin cibiyoyin lura da mata da Æ™anana yara guda 10. An fitar da jimillar 516, 554, 752. 00 a matsayin biyan kuÉ—in siyan kayayyakin. 

Alhaji Mas’ud AbdulÆ™adir ÆŠanguruf ya kasance cikakken mai goyon bayan jam’iyyar PDP wanda ya bayar da gudunmawa mai tsoka ga yaÆ™in neman zaÉ“en É—an takarar shugaban Æ™asa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar a 2019. Shi ne ya kafa Æ™ungiyar goyon bayan Atiku a jihar Katsina ta ÆŠanguruf. ÆŠan kasuwan haifaffen jihar Katsina ya koma APC ne a shekarar 2022 ta hannun gwamnan Zamfara mai barin gado Bello Matawalle.

Rukunin kamfanonin ÆŠanguruf na daga cikin manyan kamfanoni biyar da Gwamna Matawalle ke amfani da su wajen gudanar da ayyukan bogi, musamman gine-gine, saye da sayarwa na kayayyaki.

Kamfaninsa na Ɗanguruf Pharmaceutical Limited ya samu kwangilar gina masaukin Gwamna a ƙaramar hukumar Bukkuyum, a kan jimillar kudi naira 59, 141, 575. 00. An cire naira 35, 608, 185.13 daga baitul malin gwamnati aka kuma miƙa wa Mista Abdulƙadir domin wani aiki da har yanzu bai fara ba.
A ranar 22 ga watan Disamba 2022, an fitar da jimillar kuÉ—i naira 83, 878, 092. 62 daga asusun jihar Zamfara zuwa kamfanin ÆŠanguruf Pharmaceutical Limited a matsayin kuÉ—in gyaran manyan asibitoci guda 10. Ba a bayyana sunaye da wuraren da manyan asibitocin suke ba.

Bugu da ƙari, a ranar 26 ga Disamba, 2022, Gwamna Matawalle mai barin gado ya saki jimillar kuɗi naira 1, 409, 435, 798.00 ga Ɗanguruf Pharmacy LTD a matsayin biyan kuɗin siyan kayan aikin asibiti ga asibitoci 10 da ba a bayyana ba. An bayar da kuɗaɗen ne ba tare da wani bayani kan sunaye da wuraren asibitocin da za a sayawa kayan aikin ba.

Wani babban ma’aikacin ma’aikatar lafiya ta jihar Zamfara da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa halin da É“angaren lafiya ke ciki a jihar ya yi muni matuÆ™a da ban tsoro. Ya koka kan lalacewar ababen more rayuwa, rashin Æ™wararrun ma’aikata, da rashin wadatar magunguna. 
Ya kuma nuna matuÆ™ar damuwarsa kan makomar fannin lafiya a jihar. “Halin da ake ciki yana da ban tsoro, yana nan a cikin kundi yadda aka kashe biliyoyin kuÉ—aÉ—e da sunan gyara, sabuntawa, sayan kayayyakin aiki, da kuma samar da magunguna. Amma komai sake taÉ“arÉ“arewa yake yi a kullum.

“Gwamnatin da za ta zo a Zamfara tana da babban aiki ja a gabanta; domin binciken kwangilolin da aka bayar da kuÉ—aÉ—en da aka fitar. Sama da kashi 90% na ayyukan da ake yi a fannin kiwon lafiya a Zamfara ayyuka ne na bogi waÉ—anda suke kawai a kan takarda ba a zahiri ba.

“Matawalle ya zaÆ™u wajen ganin ya cire sauran Naira miliyan dari biyar (500, 000, 000) cikin Biliyan Biyu (2, 000, 000, 000.00) da gwamnatin Tarayya ta biya na kayayyakin COVID-19. Ya riga da ya cire Naira 1, 500, 000, 000. Wannan wasu muhimman bayanai ne da ya kamata gwamnatin PDP mai jiran gado a jihar ta lura da kuma yin bincike sosai idan ta karÉ“i mulki a ranar 29 ga Mayu 2023." Majiyar ta Æ™ara da cewa.


Duk da haifar da koma baya sosai da ya yi a jihar Zamfara, Gwamna Matawalle mai barin gado ya koma babban birnin tarayya ya tare yana kamun ƙafa wajen ganin gwamnatin tarayya ta naɗa shi a matsayin memba a gwamnatin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Saleh Zurmi shi ne Shugaban ƙungiyar Alternative Forum na Zamfara.

No comments