Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

'Yan Arewa Sun Magantu: Yari Ne Kadai Ya Dace da Shugabancin Majalisar Dattawa Ta 10 -Kungiyar NPF

Kungiyar siyasa a Arewacin Nijeriya ta amince da bai wa tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari goyon baya a matsayin shugaban ma...


Kungiyar siyasa a Arewacin Nijeriya ta amince da bai wa tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari goyon baya a matsayin shugaban majalisar dattawa ta goma. 

Ƙungiyar mai suna 'The North-West Progressives Forum' ta gargadi zaɓaɓɓen shugaban kasa, Bola Tinubu da kada ya kuskura ya ba da dama ga sauran yankunan kasar na shugabancin majalisar. 

Kungiyar Arewa ta NPF ta ce Yari ne ya fi dacewa da zama shugaban majalisa ta 10.

Shugaban kungiyar, Nasir Danbatta da yake zantawa da manema labarai a Kaduna a ranar Asabar 29 ga watan Afrilu, ya ce arewa maso yammacin kasar tafi kowane yanki ba da ƙuri'u wa jam'iyyar APC a zaben shugaban kasa da ya gabata. 

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Kungiyar dake arewa maso yamma ta ce babu wanda ya cancanci kujerar majalisar dattawa kamar tsohon gwamnan Zamfara. 

IDAN ZA A YI ADALCI, A BA YARI SHUGABANCIN MAJALISA

Ta kuma gargadi zababben shugana kasar Nijeriya da ya tabbatar ya bai wa Abdulaziz Yari domin yankinsa ya ba da kaso mafi tsoka a cikin kuri'un da aka kada. 

Kungiyar ta ce rashin adalci ne kawai zai sa a bai wa wani yanki na kasar nan shugabancin kujerar. 

Inda ya ce: "Muna bukatar a bamu shugaban majalisar dattawa a wannan yanki namu, kuma wanda muke so ya jagoranceta shi ne tsohon gwamnan jihar Zamfara" 

"Sakamako ya tabbatar da cewa arewa maso yamma ne yankin da yafi kowane bai wa Tinubu kuri'u wanda hakan ya sa suka fi cancanta a ba su wannan kujera", inji kungiyar.

"Duk da bama tsammanin Tinubu zai bai wa wani yanki wannan kujera, muna tunanin bai wa yankin arewa maso yamma shi ne adalci ga mutane da suka sha wahala." 

No comments