Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Yan Bindiga Sun Kashe Manoma Tara A Jihar Kaduna

Akalla manoma tara ne ‘yan bindiga suka kashe a Unguwar Danko kusa da kauyen Dogon Dawa a yankin Birnin Gwari a Jihar Kaduna, ka...


Akalla manoma tara ne ‘yan bindiga suka kashe a Unguwar Danko kusa da kauyen Dogon Dawa a yankin Birnin Gwari a Jihar Kaduna, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.

Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar a lokacin da wadanda abin ya shafa ke aiki a gonakinsu.

Mazauna yankin sun ce ‘yan bindigar sun yi awon gaba da wasu manoma kusan uku zuwa wani wuri da ba a san ko ina bane.

Zababben mamba mai wakiltar mazabar Kakangi, Yahaya Musa, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce duk wadanda aka kashe manoma ne, kuma wadanda suka samu raunukan harbin bindiga an garzaya da su asibiti domin yi musu magani.

Ya bayyana cewa wasu daga cikin mutanen kauyen kuma sun fuskanci ‘yan bindigar wanda hakan ya sa wasu suka samu raunuka daga harbin bindiga.

Har yanzu dai gwamnatin jihar ba ta mayar da martani kan lamarin ba amma jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Mohammed Jalige, ya yi alkawarin yin karin bayani nan gaba.

No comments