Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

'Yan Bindiga Sun Sace Mutum 25 A Wata Majami'a A Kaduna

  Wasu `yan bindiga sun kai hari kan wani Coci da ke karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya inda suka sace mutum akal...

 


Wasu `yan bindiga sun kai hari kan wani Coci da ke karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya inda suka sace mutum akalla 25.

Lamarin dai ya auku ne a ranar Lahadin da ta wuce lokacin da mutanen suke ibada a Cocin.

Shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya reshen jihar Kaduna, Reverend John Hayap ya tabbatar wa BBC aukuwa lamarin inda ya ce mutum 40 aka sace kafin daga bisani mutum 15 sun kubuta.

Kakakin rundunar `yan sanda a jihar Kaduna, ya tabbatar wa da kamfanin dillancin labarai na AFP aukuwar lamarin amma bai yi karin bayani ba a kan batun.

No comments