Daga Muhammad A. Dalhatu Jaridar MADOGARA ta labarto cewa; Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC, ta bayyan...
Daga Muhammad A. Dalhatu
Jaridar MADOGARA ta labarto cewa; Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC, ta bayyana cewa tana binciken gwamna Bello Matawalle kan satar sama da Naira biliyan 70 daga jihar Zamfara.
Babban jami'in hukumar ta EFCC, Osita Nwajah ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a yayin da yake jawabi ga manema labarai a hedikwatar hukumar da ke Abuja.
Sanarwar ta zo ne kwanaki kadan bayan Gwamna Matawale ya yi kokarin wofintar da binciken inda ya zargi hukumar yaki da cin hanci da rashawa da nuna bangaranci da kuma rashawa.
Mista Matawalle ya ce ya kamata EFCC ta kuma binciki mutanen da ke aiki tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari ciki har da ministocin gwamnatin tarayya.
An zargi ofishin yaki da cin hanci da rashawa da nuna tsoro da rashin kwarin guiwa wajen binciken mutanen da ke biyayya ga shugaban kasa, kuma a kwanakin baya Mista Matawalle ya caccaki Mista Buhari da cewa ba ya biyayya ga jam’iyyar APC mai mulki kuma shi ne ke da alhakin gazawar da jam’iyyar ta samu a wasu jihohin kasar a zaben da ya gabata.
Hukumar EFCC ta yi watsi da zargin nuna son kai wajen gurfanar da masu cin hanci da rashawa gaban kuliya, inda ta ce Mista Matawalle yana kokarin kawar da hankalin hukumar ne daga ayyukanta.
Karin bayani na nan tafe.
No comments