Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya bayyana tsohon maigidansa Umaru 'Yar'adua a matsayin shugaba maras son zuciya. Ya bayy...
Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya bayyana tsohon maigidansa Umaru 'Yar'adua a matsayin shugaba maras son zuciya.
Ya bayyana haka ne a wani ɓangare na ranar cika shekara 13 da rasuwar tsohon shugaban ƙasar na Najeriya.
Jonathan ya kasance mataimakin Umaru Musa Yar’Adua daga shekara ta 2007 zuwa 2010
A wani saÆ™o da ya wallafa a shafinsa na Tuwita ranar Juma'a, Jonathan ya rubuta cewa, “A wannan rana shekara 13 da ta wuce, Æ™asarmu ta yi rashin gawurtaccen shugaba maras son zuciya, Shugaban Æ™asa Umaru Musa Yar’Adua.
Mutum ne mai son zaman lafiya da adalci da kuma kamanta gaskiya.
“Muna waiwaye baya don nuna godiya ga Allah saboda rayuwarsa da kuma gudunmawar da ya bayar ga Æ™asarmu.
“Shugaba Yar’Adua, jagora ne abin misali, wanda ya rayu ba tare da nuna bambancin Æ™abilanci ko na addini ba. Kuma gudunmawarsa a fagen aikin gwamnati ta zaburas da mutane da yawa kan hanyar alheri.
“A yau, muna tuna shi da kuma hidimar da ya yi a rayuwarsa da jajircewa da duÆ™ufa wajen tabbatar da dunÆ™ulalliyar Æ™asa daya mai bunÆ™asar arziÆ™i.
Goodluck Jonathan ya ce: “Za mu ci gaba da tunawa da shi saboda gagarumin ci gaban da ya kawo da kuma himmarsa wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban Najeriya”.
No comments