Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Za Mu Sa Cin Hanci Da Rashawa Ya Zama Abin Ƙyama, In Ji Tinubu

Daga Ammar M. Rajab  Zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ce gwamnatinsa za ta samar da abubuwan ƙarfafawa da k...


Daga Ammar M. Rajab 

Zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ce gwamnatinsa za ta samar da abubuwan ƙarfafawa da kuma tsare-tsare da za su sa cin hanci da rashawa ya zama abin ƙyama ga Alƙalai da sauran ma’aikatan Nijeriya.

Hakan ya fito ne a wata sanarwa da ofishin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa ta fitar ɗauke da sa hannun Abdulaziz Abdulaziz, inda ta ruwaito Tinubu na yin wannan alƙawarin ne a ranar Alhamis a garin Fatakwal na jihar Ribas, a yayin ƙaddamar da rukunin kotunan majistare.

Taron na cikin ziyarar kwanaki biyu da Tinubu ya kai jihar domin ƙaddamar da ayyukan da gwamnatin Nyesom Wike ta aiwatar.

Tinubu ya ce tare da samar da ingantattun abubuwan ƙarfafawa waɗanda za su ba da tabbacin yanayin aiki mai kyau da kuma tsare-tsare waɗanda za su sauƙaƙa wa ma'aikata samun wuraren karɓar lamuni domin biyan muhimman buƙatu, fitinar cin hanci da rashawa za ta ragu.

“Ba za ku tsammaci Alƙalanku su rayu cikin rashin jindaɗi ba, su kuma gudanar da aiki cikin matsi, su kuma yanke hukunci cikin ƙunci. Wannan na daga cikin sauye-sauyen da suka wajaba. Dole ne mu yaƙi cin hanci da rashawa amma kuma dole ne mu kalli wani ɓangare na abin da ke haifar da hakan.

“Idan ba kwa son Alƙalanku su yi almundahana, to ku kula da jin daɗinsu. Kar ku yarda su yi aiki cikin yanayi mai haɗari," ya ce.

Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar ya ce rashin samun lamuni na ma’aikata wanda ka iya sauƙaƙa wa ma’aikata samun ƙadarori kamar gidaje da motoci ka iya sanyawa cikin sauƙi a faɗa rashawa.

“Idan kuna da hanyar karbar lamuni wannan zai rage yiwuwar cin hanci da rashawa. Ba ma son Alƙalan mu su riƙa bayar da kai bori ya hau, suna haɗa kai wajen danne adalci. Na yi alƙawarin za mu sake duba dukkanin waɗannan a tsari mai zurfin tunani".

Tinubu ya kuma jaddada ƙudurinsa na tabbatar da haɗin kan Nijeriya tare da yin alƙawarin yin adalci ga kowa.

“Haɗin kan ƙasar nan ba abin da za a yi wasa da shi bane. Abin da ni da Wike muke haɓɓakawa ke nan a tare. Na yi alƙawarin zan yi wa kowa adalci.”

Tun da farko, Gwamna Wike ya ce rukunin ya ƙunshi ɗakunan shari’a 24, ofisoshi da sauran kayayyakin aiki da nufin rage cunkoso a harabar babbar kotun jihar da kuma faɗaɗa hanyoyin samun adalci.

Ya ce gwamnatinsa ta ɗauki jin daɗin Alƙalai da kuma bunƙasa yanayin yadda kotunan suke da muhimmanci domin ganin an riƙa gaggauta gudanar da shari’a.

Wike ya bukaci ma’aikatar shari’a ta jihar da ta tabbatar da ta kula da ginin ganin yadda aka kashe masa kuɗaɗe masu yawa wajen samar da wurin.

Daga nan sai ya godewa zaɓaɓɓen shugaban ƙasar bisa yadda ya amince ya ziyarci jihar tare da ƙaddamar da ayyukan.

Bikin ya samu halartar Kakakin majalisar wakilai Rt. Hon. Femi Gbajabiamila da kuma Gwamna Muhammad Badaru Abubakar (Jigawa), David Umahi (Ebonyi), Abdulrahman Abdulrazaq (Kwara) da kuma Dapo Abiodun (Ogun).

Haka kuma waɗanda suka kasance a wurin akwai tsoffin gwamnoni da suka haɗa da Cif Bisi Akande (Osun), James Ibori (Delta), Kayode Fayemi (Ekiti), Adams Oshiomhole (Edo) da Ayo Fayose (Ekiti).

Sauran sun haɗa da ‘yan majalisar dokoki ta ƙasa, ministan wasanni da ci gaban matasa, Sunday Dare, tsohon babban lauyan gwamnatin tarayya (AGF), Mohammed Bello Adoke, SAN, shugabar mata ta jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Dr Betta Edu, Cif Ayiri Emami, da sauransu.

No comments