SAKON EASTER DAGA ZABABBEN SHUGABAN KASA Ina mika sakon gaisuwata ga mabiya addinin Kirista a Nijeriya da ma duniya baki daya w...
SAKON EASTER DAGA ZABABBEN SHUGABAN KASA
Ina mika sakon gaisuwata ga mabiya addinin Kirista a Nijeriya da ma duniya baki daya wadanda suke gudanar da bukukuwan Easter a wannan Lahadin. A yayin da muke jin daɗin wannan hutun da ya dace, ina roƙon kowanne ɗan Nijeriya da ya yi tunani a kan sadaukarwa marar iyaka da ƙauna mara yankewa da Ubangiji yake nunawa ɗan adam.
A yayin da muke wannan bikin, mu kuma tuna da wajibinmu, a matsayinmu na bayin Allah, mu Æ™aunaci maÆ™wabtanmu, ba tare da la’akari da harshe, addini da Æ™abila ba.
Ga Kiristoci a ko’ina, wannan biki na tunawa ne da irin rayuwar hidimar Yesu Kristi da hadayarsa mafi girma domin ceton ’yan Adam.
Kuma a yayin da muke bikin Easter a wannan shekara, mu rungumi muhimmancin saÆ™on hidimar Kiristi mu kuma fara Æ™aunar ’yan’uwanmu 'yan Nijeriya da gaske kamar yadda muke Æ™aunar kawukanmu.
Za mu samu ci gaba cikin sauri ta hanyar samar da zaman lafiya, hadin kai, karfi, ci gaba da wadatar da muke fata, idan muka nisanci ra'ayin raba kan jama'a, bangaranci, kabilanci da addini, muka fara rayuwar fahimtar juna da 'yan uwanmu.
Easter na nufin sabunta fata da kuma ceto. Yana kuma alamta nasarar fata akan ta yanke kauna, soyayya kan ƙiyayya da tir, da kuma kyakkyawan fata kan son zuciya. Mu rungumi wannan ruhi, mu sake sadaukar da kanmu ta hanyar ayyukan raya kasa da kishin kasa domin maslahar al'ummarmu.
Ina yi muku barka da bukukuwan Easter.
Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Zababben shugaban kasar Tarayyar Nijeriya.
08 Afrilu, 2023.
No comments