SAKON GOYON BAYA DAGA ZABABBEN SHUGABAN KASA ZUWA GA MA'AIKATAN NIJERIYA A RANAR MA'AIKATA TA DUNIYA Ina bin sahun saur...
SAKON GOYON BAYA DAGA ZABABBEN SHUGABAN KASA ZUWA GA MA'AIKATAN NIJERIYA A RANAR MA'AIKATA TA DUNIYA
Ina bin sahun sauran kasashen duniya da sauran 'yan kasa domin taya ma’aikatan Nijeriya murnar zagayowar ranar ma’aikata ta duniya ta bana. Yau rana ce ta musamman a mafi yawan kasashen duniya, rana ce ta jinjina da karramawa ga ma'aikata wanda kwazonsu da guminsu ke ci gaba da jan ragamar ci gaba da bunkasar bil'adama.
Yau rana ce mai muhimmanci ta fuskoki da yawa. Rana ce da aka ƙirƙira kuma aka samar da ita daga gwagwarmayar neman haƙƙin ma'aikata da adalcin zamantakewa da tattalin arziki. Tun daga shekarar 1891, ana bikin wannan rana a duk faɗin duniya.
A Nijeriya, kowacce ranar 1 ga Mayu rana ce ta musamman a kalandar kasarmu. Hutun da muke yi a ranar ba wai kawai domin tunawa da gudunmawa da sadaukarwar da ma’aikata suke bayarwa bane domin ci gaban kasarmu. Yana ma kasancewa baki daya a matsayin bikin kwatar haƙƙin ma'aikata domin mutunta su, ingantaccen albashi da rayuwa mai kyau, kuma abu mafi mahimmanci, shaida ce ga irin muhimmiyar rawar da ƙungiyoyin kwadago ke takawa a cikin matakan mu na samun ƙasa mai ƙarfi, haɗin kai da wadata.
Tun a shekarar 1945 lokacin da ma'aikatan jirgin kasa da wasu kungiyoyin ma'aikatan gwamnati 16 suka jagoranci yajin aikin farko na neman karin albashi sakamakon tsadar rayuwa, kungiyar kwadago a Nijeriya ta ci gaba da yaki domin kare muradun talakawan kasarmu. Ba abin mamaki ba ne cewa kungiyar kwadago ta kara samun karsashi, kuzari da karfi ga gwagwarmayar neman ‘yancin kai ta hanyar hada kai da masu kishin kasa irin su Nnamdi Azikwe, Herbert Macaulay, Ahmadu Bello, Obafemi Awolowo, Ernest Ikoli da Anthony Enahoro da sauransu.
Har ila yau ba a samu kungiyar kwadago ta Nijeriya da gazawa ba a lokacin da ake gwagwarmayar maido da mulkin dimokuradiyya. Kungiyar Kwadago ta Nijeriya da kungiyoyin da ke karkashinta - NUPENG, Textile Union, PENGASSAN, da dai sauransu sun hada kai da shuwagabanni da kungiyoyi masu fafutikar tabbatar da tsarin mulkin dimokuradiyya a Nijeriya a shekarar 1999 bayan kusan shekaru ashirin ba tare da tangarda ba na mulkin kama-karya na sojoji.
A wannan rana ta musamman, a matsayina na zababben shugaban kasa, ina mika hannun abokantaka ga ma’aikatan Nijeriya ta hanyar kungiyoyin kwadago guda biyu – kungiyar kwadago ta Nijeriya ta NLC da TUC. Za ku same ni amintaccen abokin tarayya kuma abokin aiki a yakin neman adalci na zamantakewa da tattalin arziki ga dukkan 'yan Nijeriya, gami da dukkan ma'aikata.
Yaƙinku zai kasance yaƙina domin a koyaushe zan yi muku yaƙi. Shirye-shiryena domin inganta walwala da yanayin aiki a bayyane suke a cikin kundina na sabunta fata domim Inganta Nijeriya. Alkawari ne da ya samu ta hanyar imani kuma na shirya na kiyaye.
A daidai wannan lokaci, dole ne na tunatar da ma'aikatan Nijeriya cewa dukkanninmu muna da abin hari guda da ya kamata mu tunkara, wanda dole ne mu yi nasara a tare. Shi ne yaki da talauci, jahilci, cututtuka, rashin hadin kai, kiyayyar kabilanci da ta addini da dukkanin wani mummunan karfi da ke barazana da zaman lafiya da ci gaban kasarmu.
A Nijeriya zan sami damar karramawa da alfarmar shugabanci daga ranar 29 ga Mayu, ma'aikata za su sami fiye da mafi karancin albashi. Za ku sami isasshen albashi mai dorewa domin samun rayuwa mai kyau da wadata iyalanku.
Kwanaki masu zuwa, duk da haka, za su buƙaci kyakkyawar fahimta da haɗin kai daga kowanne bangare, domin shugabanci zai buƙaci mu ɗauki tsattsauran mataki domin al'ummarmu da ma'aikatan Nijeriya su sami rayuwa mai yalwa.
Ina yiwa ma'aikatan Nijeriya da shugabannin NLC da TUC barka da ranar ma'aikata!
Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Zababben shugaban kasar Tarayyar Nijeriya,
Mayu 1, 2023
No comments