Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Zan Yi Koyi Da Shugaba Irin Umaru Musa 'Yar'aduwa -Tinubu

  Daga Ammar M. Rajab Zababben shugaban kasar Nijeriya, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya ce a yayin da yake shirin karbar ragamar shugabancin Ni...

 

Daga Ammar M. Rajab

Zababben shugaban kasar Nijeriya, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya ce a yayin da yake shirin karbar ragamar shugabancin Nijeriya a ranar 29 ga watan Mayun 2023, zai yi koyi da shugabannin irin Marigayi Umaru Musa 'Yar'adua. 

Bola Ahmad Tinubu ya bayyana hakan ne a cikin wata wasika da ya wallafa a shafinsa na Twitter, inda ya fara da cewa; "a yau, kamar kullum, ina tunawa da abokina kuma ɗan uwana na ƙwarai a fafutikar tabbatar da dimokuraɗiyya da shugabanci na gari a Nijeriya, Marigayi Shugaba Umaru Musa 'Yar'aduwa, wanda ya rasu a rana irin ta yau shekaru 13 da suka gabata".

Ya ci gaba da cewa; "Mayu 5, 2010 mai yiwuwa ya daɗe da wucewa, amma ga wasunmu, raunin har yanzu sabo ne fil. Muna tunawa da ranar kamar yadda muke tunawa da rayuwa mai albarka da Mallam Umaru Yar'adua ya yi".

Zababben shugaban kasar ya kara da cewa; "a matsayin aboki kuma abokin siyasa ina girmama abubuwan tunawa da suka faru na gaskiya, jajircewa, kishin ƙasa da nagartar aikin gwamnati wanda Marigayi 'Yar'aduwa ya nuna a matsayin gwamnan jihar Katsina (1999 zuwa 2007) da shugaban Nijeriya (2007 zuwa 2010).

"A yayin da nake shirin karɓar ragamar shugabancin ƙasar nan a ranar 29 ga watan Mayu, na ƙuduri aniyar yin koyi da nagartattun shugabanni irin su Malam Umaru ‘Yar’aduwa wanda ya nuna dabi’u na musamman da suka cancanta na nagarta da kuma sadaukar da kai ga ƙasarmu.

"Ka huta ɗan uwa. Allah ya sa ruhinka ya ci gaba da kasancewa cikin salama a wurin Ubangijinka, Ameen", ya karkare da addu'a.

No comments